A jawabinsa yayin bikin sanya hannun, jami'in hulda da jama'a na kamfanin Whale Rock, Manfred Uxamb, ya bayyana cewa, tuni aka kammala aikin safiyo da na farar kasar da za a rika amfani da ita wajen samar da simintin.
A cewarsa, akwai farar kasar da kamfanin zai iya amfani da ita har zuwa sama da shekaru 40 a wurin da ake saran kafa kamfanin, wadda ake fatan zai samar da sama da dala biliyan 30 ga tattalin arzikin kasar.
Bayanai na nuna cewa, kamfanin na kasar Sin yana da ma'aikata 6,000 da kuma kwarewar aikin samar da Siminti ta sama da shekarau 30.
Kamfanin da ake fatan kafawa mai nisan kilomita 245 daga birnin Windhock, babban birnin kasar zai kasance na biyu mafi girma a kasar ta Namibia bayan kamfanin Ohorongo da ke samar da sama da tan 500,000 na Siminti a shekara.
Kamfanin zai samar da guraben ayyukan yi 400 da zarar ya fara aiki.
Jakadan Sin a Namibia Xin Shunkang da shugaban kamfanin mai kula da harkokin Asiya da Afirka Zhang Jimin na daga cikin wadanda suka halarci bikin rattaba hannun.(Ibrahim)