A yayin ziyarar da shugaban Sin Xi Jinping ke yi a kasar Birtaniya, a jiya Litinin bisa agogon wurin, an gudanar da taron shawarwari game da makamashi tsakanin Sin da Birtaniya na shekara-shekara karo na 4 a birnin London, inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar nazari da kirkire-kirkire ta Sin da Birtaniya.
An ba da labari cewa,tuni gwamnatin Burtaniya ta samar da kasafin kudi da wannan shiri, wanda zai zama abin koyi wajen yin nazari da hadin gwiwa a fannin fasahar nukiliya tsakanin Sin da kuma kasashe masu sukuni.(Fatima)