Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Gaoli, ya gana da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma a Talatar nan, yayin ziyarar aiki da ta kawo nan birnin Beijing.
Mista Zhang ya ce, Sin na fatan kara hadin gwiwa da AU, don tabbatar da shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a yayin taron kolin kiyaye zaman lafiya na MDD dangane da baiwa AU tallafin aikin soja, da sa kaimi ga ayyukan zirga-zirga da samar da manyan ababen more rayuwa a nahiyar, tare kuma da raya karfin samar da kayayyaki.
A nata bangare, Zuma bayyana godiya ta yi game da goyon baya da Sin ke nunawa AU, da kasashen Afrika wajen cimma burin wanzar da zaman lafiya. Ta ce AU na fatan kara hadin gwaiwa da Sin, domin cimma nasarar karbar bakuncin taron koli na tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika, wanda ake shirin gudanarwa a birnin Johannesburg, matakin da ake fatan zai tallafa wajen sa kaimi ga samun ci gaba ta fuskar hadin gwiwa tsakaninsu. (Amina)