Jiya Alhamis ne aka bude wani taro bisa jagorancin MDD kan horas da masu shiga tsakani kan harkokin cinikayya daga kasashen nahiyar Afrika dake magana da harshen Turanci a Nairobin kasar Kenya, karkashin kungiyar kula da aikin yankin ciniki maras shinge na Afirka wato CFTA.
Taron wanda za'a shafe mako guda ana gudanarwa, kuma na hadin gwiwa ne tsakanin kwamitin MDD mai lura da cigaban kasuwanci da hukumar kungiyar hadin kan Afrika ta AU, zai mai da hankali ne wajen samar da dabaru ga masu shiga tsakani na Afrika gabanin kafuwar yankin ciniki maras shinge ta Afirka ta CFTA a shekarar 2017.
A jawabinta na bude taron, Darakta mai kula da harkokin cinikayya da masana'antu ta hukumar AU Madam Maphanga, ta ce nahiyar Afrika ta dora muhimmanci sosai kan cigaban yankin CFTA, tun lokacin da aka cimma daidaiton kaddamar da yankin na CFTA a taron koli na AU da ya gudana a watan Yuni.
A cewar Maphanga, taron zai taimaka wajen karfafa dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar Afrikan da kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO.( Ahmad Fagam)