in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta jinjina ma dabarun hadin gwiwa na Sin a Afrika
2015-09-09 11:14:37 cri
Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta jinjina ma dabarun da kasar Sin take dauka wajen hadin gwiwwa na zaman lafiya a nahiyar.

Kwamishinan zaman lafiya da tsaro Smail Chergui da kuma shugaban ayyukan din din din na kasar Sin a kungiyar Kuang Weilin a ranar litinin din nan suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniya, inda kasar Sin za ta ba da taimakon kudi har dala miliyan 1.2 don raya ayyukan kungiyar aiki ta musamman da AU ta tura ga kasar Somaliya wato AMISOM.

Kwamishina Chergui ya gode ma kasar Sin saboda wannan taimako, yana mai tuna baya kan yadda gwamnatin kasar Sin ta bada gudunmuwa na dala miliyan 2 a shekara ta 2014 domin bada taimako ga ayyukan kungiyar AU wajen yaki da cutar Ebola a yammacin Afrika.

Har ila yau Smail Chergui ya ce, kasar Sin ta sake bada wani taimakon kudin na dala miliyan 1.2 ga asusun ayyukan kiyaye zaman lafiya a nahiya a watan Janairun bana.

Ya ce, wannan gudunmuwa na baya bayan nan zai taimaka matuka wajen inganta kokarin sojin kasashen nahiyar a cikin ayyukan kiyaye zaman lafiya da suke yi a Somaliya.

A nashi jawabin Kuang Weilin ya tabbatar ma kwamishinan cewa, Sin za ta ci gaba da goyon bayan Afrika, musammn yadda nahiyar ke kokarin ganin ta raba kanta da duk wani tashin hankali, ta kuma samu kyakkyauwan cigaba da yalwata ga al'ummarta.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China