Shugabannin nahiyar sun bayyana hakan ne yayin taron koli na kungiyar AU karo na 25 da ya kammala a kasar Afirka ta Kudu.
Da yake tsokaci game da hakan, jagoran taron, kuma shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya ce taron na wannan karo ya samar da damar tattauna batutuwa da dama, musamman wadanda suka shafi harkokin siyasa, da tattalin arziki, da kuma na zamantakewar al'ummar nahiyar.
Mugabe ya ce taron ya amince da hada karfi-da-karfe, wajen yaki da kungiyoyin tada-kayar baya. Ya kuma jinjinawa kungiyar AU bisa kaddamar da yarjejeniyar kafa yankin cinikayya cikin 'yanci a nahiyar.
Kaza lika shugaban na Zimbabwe, ya ce shugabannin AUn sun amince da aiwatar da matakan cimma muradun nahiyar Afirka nan da shekarar 2063, matakin da zai taimaka wajen cimma burin raya tattalin arzikin nahiyar cikin dogon lokaci. Wadannan muradu dai sun hada da kafa yankin cinikayya cikin 'yanci, da samar da layukan dogo domin jiragen kasa masu saurin gaske, da hadin gwiwa wajen samar da cibiyar yaki da cututtuka ta nahiyar, tare kuma da kafa jami'ar kawancen kasashen na Afirka.