A ranar 15 ga wata, yayin da Mista Zhang ke ganawa da shugabar hukumar zartaswa kungiyar AU Nkosazana Clarice Dlamini-Zuma, ya mika sakon taya murna da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa taron koli na kungiyar AU a wannan karo, inda ya ce, a halin da ake ciki yanzu, hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika na samun babbar dama, akwai makoma mai haske wajen raya shi. Kana, Sin na gaggauta inganta hadin gwiwa da kasashen Afrika, don cimma burin raya hadin gwiwa a fannonin sufuri da kayayyakin more rayuwar jama'a, da tattauna matakan da za a dauka a fannin kiwon lafiya don hana yaduwar cutar Ebola.
A nata bangare, Madam Zuma ta gode wa shugaba Xi da ya mika sakon taya murna ga taron, kuma ta ce, kungiyar AU tana sa ran ci gaba da karfafa hadin gwiwa a fannonin sufuri da kayayyakin more rayuwar jama'a, da kiwon lafiya, da aikin gona, da horar da ma'aikata, da samar da zaman lafiya da karko da sauransu, don cimma burin samun moriyar juna.(Bako)