in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan na kasar Afirka ta Kudu
2015-06-15 20:28:34 cri
Wasu rahotannin baya bayan nan na cewa shugaba Omar al- Bashir na kasar Sudan, na ci gaba da kasancewa a kasar Afirka ta kudu, duk kuwa da kasancewar wata kotun kasar na sauraron karar da aka shigar gabanta, domin neman izinin bada sammacen cafke shi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an gano shugaban kasar ta Sudan a harabar wani Otel, wanda ke kusa da babban dakin taro na Sandton, inda shugabannin kungiyar AU ke gudanar da taro karo na 25.

Sai dai wasu rahotannin na daban na cewa tuni jirgin shugaba Al-bashir ya tashi, daga wani filin tashin jirage dake birnin Pretoria dauke da shugaban na Sudan.

Kawo yanzu dai babu wata kafa da ta tabbatar da wadannan labarai a hukunce.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China