Mr. Mbeki wanda ya jagoranci tawagar ta AU, a yayin ziyarar da suka kaiwa shugaba Omar al-Bashir na Sudan a jiya Litinin, ya shaidawa 'yan jarida cewa daya daga muhimman batutuwan da suka zanta da shugaba Al-Bashir akai shi ne batun aniyar kasashen biyu, na wanzar da tsaro a kan iyakokin su.
Ya ce don gane da hakan ne ma kwamitin sa, ke shirin kiran wani taro na masu ruwa da tsaki a fannin siyasa da tsaron kasashen biyu, da nufin tabbatar da kafuwar wannan yanki mai muhimmanci.
A daya bangaren kuma, mataimaki ga shugaban kasar Sudan Ibrahim Mahmoud Hamid, ya bayyana aniyar kasar sa na aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da kasashen biyu suka rattabawa hannu a shekarar 2012. Ya ce Sudan ta amince da tsarin kungiyar AU na kafuwar yanki maras makamai, koda yake a cewar sa, da fari Sudan ta Kudu ta amince da wancan tsari, kafin daga bisani ta sauya matsaya, lamarin da ya gurgunta burin cimma nasarar kafuwar yankin. (Saminu Alhassan)