in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na taka muhimmiyar rawa a fannin gina ababen more rayuwa a Afrika
2015-06-14 14:14:54 cri
Sakataren zartaswa na sabon tsarin dangantakar abokantaka na Afrika (NEPAD), Ibrahim Maiyaki, ya bayyana a ranar Asabar a birnin Johannesburg cewa kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a cikin cigaban gine ginen ababen more rayuwa. Shirin NEPAD wani tsari ne na cigaba da wasu shugabannin Afrika suka kafa a karkashin jagorancin tarayyar Afrika (AU).

Kasar Sin tun tuni ta taka muhimmiyar rawa domin yawancin shirye shirye a fannin gina ababen more rayuwa kasar Sin ce ta zuba kudin gina su.

Yanzu, muna bukatar kawai kawo gyara kan samun kudade manyan ayyukan shiyyoyi, in ji mista Mayaki, tsohon faraministan kasar Nijar, a yayin taron kungiyar AU karo na 25 a birnin Johannesburg. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China