in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU na shirya kafa kotun Afirka
2015-06-13 13:31:28 cri
Jiya Jumma'a 12 ga wata, shugaban sashen ba da shawara kan harkokin doka na kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta AU Vincent Nmehielle ya bayyana cewa, kungiyar AU na shirya kafa wani kotun Afirka, domin gudanar da bincike na musamman kan shugabannin kasashen Afirka da ake zargi da laifin yaki da cin zarafin dan Adam, kuma domin shirya ma wannan aikin, da farko, kungiyar AU za ta kafa wani kotun musamman a kasar Senegal cikin watanni shida masu zuwa, domin sauraron karar tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre.

A yayin taron maneman labarai da aka yi a wannan rana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, Vincent Nmehielle ya ce, alkalai guda biyu da suka zo daga kasar Senegal, dayan daga wata mambar kasar kungiyar AU da kuma wata tawagar dake kunshe da masu taya alkali yanke hukunci guda uku za su sauraron karar Hissene Habre, kuma za a fara aikin a watan Yulin bana.

Bugu da kari, ya ce, wannan zai kasance karo na farko da kungiyar AU za ta saurari karar wani tsohon shugaban wata kasa a Afirka da ake zargi da aikata laifin yaki da cin zarafin dan Adam da kanta, idan za a iya cimma nasarar sauraron karar Hissene Habre, za a fara sauraro sauran kararrakin da suke yin kama da haka, kuma a nan gaba, ba za a gabatar da shugabannin kasashen Afirka da aka zargin aikata laifin yaki da cin zarafin dan Adam gaban kotun Hague, domin gudanar da bincike a kansu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China