in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Al-Bashir ya yi fice daga Afirka ta Kudu
2015-06-15 21:02:55 cri
Fadar gwamnatin kasar Sudan ta tabbatar da cewa shugaba Omar Al-Bashir ya tashi daga kasar Afirka ta Kudu zuwa birnin Khartoum, bayan da ya halarci taron kungiyar AU karo ba 25.

Kakakin gwamnatin Sudan Ahmed Bilal Osman, ya ce ana sa ran isar shugaba Al-Bashir gida da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Litinin din nan bisa agogon birnin Khartoum.

Zuwan shugaba Al-Bashir Afirka ta Kudu dai ya yamutsa hazo, tun bayan da kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC ta daga bukatar mika mata shi, bisa zargin da take masa na aikata laifukan yaki a yankin Dafur dake kasar ta Sudan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China