Shugaban kwamitin kula da harkokin tattalin arziki, al'umma da al'adu na kungiyar AU Joseph Chilengi ya zargi kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya da neman a cafke shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir a yayin taron kolin kungiyar AU karo na 25 da har yanzu ake gudanarwa a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, ya ce, hakan ya karya dokar kariyar diplomasiyya.
Bayanai na nuna cewa, umarnin kotun na neman gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta cafke shugaban Sudan ya karya dokar kasa da kasa da abin ya shafa.
A ranar Lahadi ne aka bude taron kolin kungiyar AU karo na 25 a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu. Kotun kolin birnin Pretoria ta kasar Afrika ta kudu ta ba da umurnin hana Omar Al-Bashir ya bar kasar, sabo da kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya ta nemi kasar ta cafke shugaban kasar Sudan da kotun ta ICC ke nema ruwa a jallo.
Amma a jiya Litinin, Omar Al-Bashir ya koma birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan daga kasar Afrika ta kudu ta jirgin sama na musamman.(Lami)