in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban baje da koli na kayayyaki ya bayyana al'adun Afrika lokacin ranar AU
2015-09-12 13:22:04 cri

Bikin baje koli da aka yi tare da sayar da kayayyaki cikin rahusa ya bayyana al'adun Afrika, salon adonsu da kide-kidensu a lokacin bikin ranar Kungiyar tarayyar kasashen Afrika na AU.

Bikin da aka shafi kwanaki 4 ana yinsa a tsakanin ranar 9 zuwa 12 ga wannan wata yana daga cikin ayyukan murnar ranar kungiyar AU a cibiyar kungiyar dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

An bayyana al'adun Afrika mafi kyau a rumfuna da suka kware wajen kayayyakin hannu da suka hada da kayan wuya, zannuwan atamfa, adabin Afrika, kayayyakin da aka dinka da hannu, kayayyakin kwalliya , magungunan gargajiya da kayayyakin sassaka na nahiyar.

A lokacin da take kaddamar da bikin a hukumance, kwamishinar kungiyar ta AU a bangaren ciniki da kasuwanci Fatima Acyl ta yaba da rawar da iyayen kasa na nahiyar suka taka wajen samun 'yancin nahiyar, inda ta tunar da cewar, hangen nesansu na samar da 'yancin Afrika da walawarsu har yanzu shi ne babban jigo na tsarin al'adu na hadin kan Afrika.

Ta ce, don haka, babban baje koli na kungiyar AU ya zama wani tubali na habaka kasuwancin Afrika wanda ya kawo manya da kananan ciniki a kasar ta Habasha, kuma ya bada sarari a gare su wajen inganta nasu kayayyaki da kuma yi mu'amala da juna.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China