Makasudin atisayen soji na wannan karo shi ne warware matsalolin tsaro na Afrika bisa karfin kanta, da tantance kwarewar rundunar ASF ta Afrika, don cimma burin gudanar da aikin soji daga duk fannoni kafin watan Disambar shekarar bana.
Rundunar ASF za ta kunshi sojoji 25000 da suka fito daga kasashen yammacin Afrika, da na arewacin Afrika, da na gabashin Afrika da kuma kudancin nahiyar, wadanda za su zama ginshikin sojojin tabbatar da zaman lafiya da karko a Afrika. Nauyin da ke wuyansu shi ne nacewa kan horaswa don mayar da martani kan shirin ko-ta-kwana. Haka zakila idan M.D.D. ko kungiyar AU suka bukace ta, za su iya gabatar da roko, don amfani da su.(Bako)