in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na matukar bakin ciki game da rasa rayuka sakamakon hadarin jirgin saman kasar Rasha
2015-11-02 20:38:10 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Hua Chunying, ta ce Sin na matukar bakin ciki game da asarar rayukan da aka samu, sakamakon hadarin jirgin saman fasinjan nan na kasar Rasha, wanda ya fadi a Masar ya kuma hallaka daukacin mutane dake cikin sa.

Yayin taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Madam Hua ta ce shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaministan Sin Li Keqiang, da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, sun bugawa takwarorin su na kasar Rasha Vlładimir Putin, da Dmitry Medvedev da Sergei Lavrov wayar tarho, inda suka isar da ta'aziya ga iyalan mamatan.

Jirgin saman na kasar Rasha samfurin A321 ya fadi ne ya kuma tarwatsa a zirin Sinai, mintuna 20 da tashin sa daga birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar, a hanyar sa ta zuwa birnin St Petersburg na kasar Rasha. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China