Takardar mai taken "Shirin Moscow" da aka gabatar a shafin intanet na ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha na kunshe da batutuwa guda 10, kana babban batu cikin wannan takardar shi ne, ya kamata bangarorin biyu da rikicin ya shafa su warware rikicin kasar Syria ta hanyar siyasa bisa ka'idojin sanarwar Geneva.
Bugu da kari, mai shiga tsakani na shawarwarin, kana shugaban cibiyar nazarin ilmin Gabas ta tsakiya ta kwalejin kimiyyar kasa ta Rasha, Vitaly Naumkin ya bayyana cewa, a yayin shawarwrin, mahatarta taron sun yi musayar ra'ayoyi cikin lumana, inda suka nuna fatansu na warware rikicin kasar Syria ta hanyar zaman lafiya. Kaza lika, bisa sakamakon da aka samu, an ce, akwai iyuwar warware rikicin kasar ta hanyar zaman lafiya. (Maryam)