in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta zargi Japan da ci gaba da nuna bambancin ra'ayi kan sakamakon yakin duniya na biyu
2015-08-23 13:41:17 cri
A jiya Asabar 22 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta ba da sanarwar yin zargi kan kasar Japan dake ci gaba da nuna bambancin ra'ayi kan sakamakon yakin duniya na biyu da kowa ya amince da shi.

Firaministan Rasha, Alexander Medvedev ya kai ziyara a tsibirin Etorofu dake tsibiran Southern Kurils a wannan rana. Gwamnatin Japan ta nuna rashin amincewarta kan wannan batu. Ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta mai da martani cewa, ko shakka babu Rasha ce ke da ikon mallakar tsibiran Southern Kurils. Kuma firaministan kasar na da ikon tsara wuraren da zai kai ziyara a Rasha, bai kamata sauran kasashen duniya su bayyana ra'ayoyinsu kan wannan batu ba.

Dadin dadawa, a wannan rana, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ba da sanarwa a shafinta na yanar gizo cewa, ra'ayin Japan kan ziyarar firaministan Rasha Medvedev a tsibirin Etorofu ya sake nuna cewa, mahukuntan Japan suna ci gaba da nuna bambancin ra'ayi kan sakamakon yakin duniya na biyu da kowa ya amince da shi.

Ban da haka, sanarwar ta ce, an hallaka rayukan mutane sama da miliyan 10 na kasashen gabashin Asiya a cikin yakin duniya na biyu. Shi ya sa irin wannan ra'ayin da Japan ta nuna a fili zai haifar da tababa cewa, ko gwamnatin Japan za ta cika alkawarinta na girmamawa ainihin tarihi da abubuwan da suka abku a cikin yakin duniya na biyu?(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China