in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha: An gudanar da faretin sojoji don tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar kare kasar
2015-05-09 17:04:17 cri

A Rasha an gudanar da gagarumin faretin sojoji, a babban filin da ake kira Red Square dake birnin Moscow, faretin da aka gudanar domin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar kare kasar daga 'yan facist.

An dai gudanar da faretin ne a yau Asabar, da misalin karfe 10 na safe bisa agogon birnin. Shugabanni daga kasashe daban-daban, da wakilan kungiyoyin kasashen duniya kimanin 30 ne suka halarci taron, ciki hadda shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Wata kafar yada labaru ta kasar Rasha ta ba da labari cewa, sojoji fiye da dubu 16, da kuma motocin yaki kimanin 200, da jiragen sama masu saukar ungulu 140 ne suka shiga faretin. An ce, rukunonin sojoji 10 daga kasashen waje ciki hadda kasar Sin, suma sun shiga wannan biki domin bayyana goyon bayan su.

Bikin da kasar ta Rasha ta shirya a wannan karo ya dara na shekarun baya, inda ta cikin sa aka gabatar da sabbin na'urorin makaman yaki da dama. Matakin da ya sanya wasu kafofin yada labaru hasashen cewa bikin na bana, ya dara makamantansa da Rashan ta taba gudanarwa, a girma da kuma kasaita a tarihin ta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China