Ofishin firaministan kasar Masar ya tabbatar a yau Asabar 31 ga wata da cewa, wani jirgin sama na kasar Rasha ya fadi a tsibirin Sinai na kasar.
An bada labarin cewa, wannan jirgin sama mai dauke da fasinjoji fiye da 200, wadanda yawancinsu masu yawon shakatawa ne 'yan kasar Rasha, ya tashi daga Sharm el Sheikh na Masar zuwa birnin Saint Peterburg na Rasha, amma bayan tashinsa ba da dadewa ba, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama na Masar ta kasa tuntubar shi .
Gidan telibijin na "Rasha na Yau" ya bada labarin cewa, hukumar tsaron Masar ta ce, babu alamar da ke cewa, an harbe wannan jirgin sama, amma kafin faduwar jirgin, matukin jirgin ya gaya wa ma'aikatan filin jirgin sama cewa, akwai matsalar fasaha a jirginsa, don haka yana son sauya hanyar jirgin ya sauka a Alkahira. (Tasallah)