Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Rasha Igor Konashenkov, ya ce harin bai shafi yankunan fararen hula ba.
Mai magana da yawun hukumar tsaron na Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce wannan hari da Rasha ta kai ta sama a Syria na wucin gadi ne, kuma za'a ci gaba da kai harin ne kadai a lokacin da dakarun gwamnatin Syria ke yin lugudan wuta a yankunan.
Peskov ya bukaci kasashen duniya da wannan lamari ya shafa da su watsa bayanai da suka shafi yaki da ta'addanci a tsakanin su.
Kasar ta Rasha ta yanke shawarar kaddamar da hare hare ta sama ne kan mayakan IS a Syria, bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da shugaba Vladimir Putin da ya yi amfani da sojojin sama wajen kai hare haren a Syria a ranar Larabar nan.
Bayan 'yan sa'o'i da kaddamar da harin na farko, fadar White House ta Amurka ta jaddada aniyar hada kai da Rasha domin kawo karshen rikicin Syria. (Ahmad Fagam)