A ran 23 ga wata, tawagogin wakilan Rasha da Ukraine sun taba yin shawarwari dangane da batun zirga-zirgar jiragen sama dake tsakanin kasashen biyu a birnin Brussels na kasar Belgium, amma bangarorin biyu ba su cimma matsayi daya ba a yayin shawarwarin.
Tun bayan barkewar rikicin Ukraine, sau da dama gwamnatin Ukraine take zargin kasar Rasha da tura sojoji zuwa gabashin kasar Ukraine domin goyon bayan 'yan tawaye, amma kasar Rasha ba ta amince da zargin na gwamnatin Ukraine.
Kana, kwanan bayan, kasar Ukraine ta fidda wata takarda domin sanya takunkumi ga kasar Rasha, wanda ya shafi wasu kamfanonin jiragen sama, bankuna, kamfanonin ciniki da kuma gidajen talabijin na kasar Rasha da dai sauransu. (Maryam)