in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara bincike kan hadarin jirgin saman Rasha da ya fado a Masar
2015-11-02 12:40:36 cri
Rahotanni sun ce yanzu haka, tawagar masu bincike na kasar Masar da sauran kasashen duniya sun fara gudanar da bincike a jiya Lahadi domin gano masabbabin faduwar jirgin saman kasar Rasha wanda ya afku a ranar Asabar a yankin Sinai na kasar Masar.

Tuni dai tawagar masu binciken na kasashen Masar da Rasha suka fara yin nazari kan bakaken akwati 2 dake cikin jirgin wadanda ke nadar bayanai aka gano su tun a ranar Asabar.

Shafin yanar gizo na Ahram ya ruwaito cewa, tawagar masu binciken ta hada da wasu kwararru biyu da suka kware kan lafiyar jirage daga kamfanin tukin jiragen saman na kasar Faransa, da kuma wasu kwararru 2 'yan kasar Jamus za su gudanar da binciken tare da jami'an na Masar da Rasha.

Tuni dai ministan kula da agajin gaggawa na kasar Rasha Vladimir Puchkov, ya isa birnin Cairo tare da tawagar kwararru domin haduwa da tawagar masu binciken ta Masar.

Kawo yanzu, ma'aikatan ceto sun gano gawawwakin mutane 163 da ta matuka jirgin, daga cikin adadin fasinjojin 224 dake jirgin, kuma an karkare aikin ceton.

Jirgin saman na Rasha ya yi hadari ne a wani yanki mai tsaunuka dake kusa da birnin Sinai, sai dai kungiyar IS ta yi ikirarin ita ce da alhakin hadarin jirgin.

Sai dai Firaiminsitan Masar Sherif Ismail, ya musanta, inda ya bayyana cewa, babu wata hujjar da za ta tabbatar da musabbabin hadarin jirgin har sai an binciki bayanan dake dauke cikin bakin akwatin jirgin.

Ismail, ya ce kwararru sun tabbatar da cewar ba zai taba yiwuwa ba a harbo jirgin a yayin da yake kololuwar sama. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China