Muna tare da imanin cewa kawancen Syria, Rasha, Iran da Iraki zai cimma babbar nasara, kuma idan hakan bai tabbata ba za a fuskanci tabarbarewar wannan shiyya baki daya, in ji shugaba Assad, yayin da yake tsokaci kan kokarin hadin gwiwa da Rasha ke jagoranta domin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria.
A yayin wata hira da gidan talabijin na Iran al-Khabar a ranar Lahadi, shugaban Syria ya bayyana cewa akwai babban kwarin gwiwar samun nasarar wannan kawance, ba wai karami ba.
Jiragen yakin Rasha sun fara kai hare hare ta sama a ranar Laraba kan sansanonin 'yan tawaye dake yankunan Syria da dama, lamarin da ya bayyana shigar Rasha a karon farko kan yaki da kungiyoyin ta'addanci a Syria.
A 'yan makwannin da suka gabata, ministan harkokin wajen Syria Walid al-Mouallem ya bayyana a wata hira cewa gwamnatinsa za ta iya neman taimakon soja daga Rasha idan akwai bukata. Daga baya, manyan jami'an Rasha sun bayyana cewa Rasha a shirye take domin taimakawa Syria.
Rasha ta kara yawaita taimakon soja zuwa sojojin Syria a baya bayan nan. Jami'an Rasha sun jaddada cewa Moscow zata cigaba da samar da taimakon soja, har ma da na kwararru ga Damascus. Tare da bayyana cewa karuwar wannan tallafin soja nada manufar yaki da ta'addanci bisa yadda dokar kasa da kasa ta tanada. (Maman Ada)