in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta soki lamarin Amurka na kin raba bayanan sirri kan Syria
2015-10-09 11:02:13 cri
Dari darin Amurka na raba bayanan sirri kan Syria ba zai kawo cikas ba ga ayyukan sojan Rasha ba a wannan kasa dake fama rikcin yaki domin hukumomin Mosco na samun bayanai sosai daga sauran wasu majiyoyi, in ji wani jami'in kasar Rasha a ranar Alhamis.

Muna samun wadannan bayanai daga sauran wasu majiyoyi daga wasu kasashe, muna daidaita wadannan bayanai tare da abokan mu a cibiyar samun bayanai ta Bagdad, in ji mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Serguei Riabkov.

Rasha, Iran, Iraki da Syria sun kafa wata cibiyar tattara bayanai a Bagdad, baban birnin Iraki, da zummar musayar bayanai tsakaninsu kan gine ginen kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria.

Mista Riabkov ya kara da cewa Washington da abokanta suna da wasu manufofinsu na daban a Syria, dake sabawa kokarin hada kan 'yan kasar Syria da ma kawo karshen rikici a wannan kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China