Reshen kungiyar IS masu tsattsauran ra'ayoyi dake kasar Masar ya sanar a jiya Asabar 31 ga watan Oktoba cewa, ya dauki nauyin hadarin faduwar jirgin sama na kasar Rasha wanda ya faru ne a wannan rana. A gabannin haka, kasashen Rasha da Masar sun tabbatar da cewa, dukkan mutanen dake kan jirgin sun rasa rayukansu.
A yanzu haka, kasashen Rasha da Masar suna kokarin binciken dalilin da ya haddasa hadarin.
Jirgin sama na Airbus kirar A321 na kamfanin Kogalymavia da ya tashi daga birnin Sharm El-Sheikh na kasar Masar zuwa birnin Sankt-Peterburg na kasar Rasha ya fadi bayan da ya tashi ba da dadewa ba jiya da sassafe. Kasashen Rasha da Masar sun tabbatar da cewa, wannan jirgin sama yana daukar mutane 224.
Firaministan kasar Masar Sherif Ismail ya bayyana jiya cewa, an samu wani akwatin nadar bayanai na jirgin. Bayan da aka yi bincike, za a tabbatar da dalilin faruwar hadarin.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ayyana ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar ta'aziyya domin tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hadarin a yankin Sinai na Masar. Har wa yau shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi ya buga mista Putin wayar tarho, inda ya nuna jejeto kan hadarin, kuma ya bayyana cewa, yana son ba da taimako bisa iyakacinsa ga kasar Rasha domin binciken wannan hadari.(Lami)