Bisa labarin da aka bayar a shafin internet na shugaban kasar Rasha, an ce, shugaba Putin ya bayyana a gun bikin taya murnar ranar sojojin ruwa a sansanin jiragen ruwan yaki na Kaliningrad dake tekun Baltic a wannan rana cewa, Rasha na alfahari da sojojin ruwa, kuma kasar Rasha kasa ce mai karfin sojojin ruwa a duniya. Don haka kiyaye matsayin kasa mai karfin sojojin ruwa shi ne babban alhakin na tun fil azal, kana za a bar gado sojoji da jiragen ruwan yaki na zamani ga zuriyoyin na gaba.
Hakazalika kuma, Putin ya ce, kasar Rasha ta gudanar da ayyuka da dama don tabbatar da karfinta na sojojin ruwa. A halin yanzu, jiragen ruwan yaki na kasar Rasha suna zarafi da karfin tabbatar da tsaron kasar da kiyaye moriyar kasar baki daya. (Zainab)