Sanarwar ta ce, kwamitin ya nuna damuwa sosai kan wasu manyan laifuffukan da aka aikata a Burundi, ciki hadda kisan kai, azabatar da mutane, kisan kare dangi, ba da kariya ga wadanda suka aikata laifuffuka da sauransu. Halin jin kai na kara tsananta a wannan kasa, lamarin da ya sa 'yan kasar kimanin dubu 200 ficewa zuwa kasashen makwabtaka. Kwamitin ya yi suka ga matakan da aka dauka a Burundi na karya hakkin Bil Adam da nuna karfin tuwo, kuma ya kalubalanci yanke hukunci kan wadanda suka aikata laifi.
Ban da haka kuma, kwamitin ya yi kira ga bangarori daban-daban na kasar Burundi da su gudanar da shawarwarin neman zaman lafiya.
Dadin dadawa, sanarwar ta ce, kwamitin ya yi maraba da shawarar da AU ta dauka na kara tura masu sa ido kan batun kare hakkin Bil Adam da masanan soja a Burundi. (Amina)