An ce, kimanin karfe 11 na daren ranar 31 ga watan Yuli, wasu dakarun dake sanya kayan soja da ba a tantance ko su waye ba sun kai hari kan wasu gidaje biyu dake gabas maso kudancin Bujumbura, babban birnin kasar Burundi, daya daga cikin mutanen biyu da dakarun suka harbe wani shugaban makarantar sakandare ne, kuma dukkansu mambobin jam'iyyar FDD mai mulki.
Haka kuma, wadannan dakaru sun kuma kai hari a wani garin dake kusa da birnin din a wannan rana da dare, lamarin da ya tilaswa mazaunan garin fice wa.
A watan Afrilun shekarar bana, jam'iyyar FDD ta zabi shugaba mai ci Pierre Nkurunziza a matsayin dan takarar shugaban kasar, lamarin da ya sa jam'iyyar adawa ta kasar ta fara yin zanga-zanga domin nuna adawa da neman wa'adin aiki na uku na shugaban kasar.
A ran 21 ga watan Yuli, an yi babban zaben shubagan kasa a Burundi, kuma a ranar 24 ga watan Yuli, hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da cewa, Pierre Nkurunziza ya lashe babban zaben da kashi 69.41 bisa 100 na kuri'un da aka jefa, kana, kotun tsarin mulkin kasar ta sanar a ran 30 ga watan Yuli cewa, Pierre Nkurunziza ya sake lashe babban zaben shugaban kasar, kuma wa'adin aikinsa zai kasance shekaru biyar. (Maryam)