Mr. Nzobonariba ya ce, gwamnatin kasar ba ta taba kin duk wani mai shiga tsakani da aka tura mata ba daga MDD. Idan har Majalissar ta aiko da sabon mai shiga tsakani za'a yi maraba da shi, sai dai a cewar shi dole a yi la'akari da dokokin kasar da yarjejeniyar kasa da kasa da kasashen da abin ya shafa suka sanya wa hannu.
A watan Mayu da Yuni, MDD ta aike da masu shiga tsakani guda biyu domin daidaita matsalar siyasa da tsaro kasar ta Burundi wanda batun zarcewa karo na uku na shugaba mai mulki na yanzu Pierra Nkurunziza ya haddasa.
Na farko shi ne dan asalin kasar Algeriya Sa'id Djinnit wanda 'yan adawa suka ki amincewa da shi bisa zargin marawa gwamnati baya. Sai na biyu kuma dan asalin kasar Senegal Abdoulaye Bathily wanda shawarwarinsa ba su samu karbuwa daga jam'iyya mai mulkin kasar da sauran magoya bayanta ba.(Fatimah Jibril)