Shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi, ya baiwa jami'an tsaron kasarsa wa'adin watanni biyu, na su kawo karshen kungiyoyi masu dauke da makamai, wadanda ke hallaka jami'ai musamman a Bujumbura fadar mulkin kasar.
Nkurunziza ya bada wannan umarni ne yayin da yake zayyana manufofin ci gaban kasarsa na shekaru 5 masu zuwa. Yana mai cewa za a bada horo na musamman ga wani rukuni na fararen hula, da jami'an tsaro, da jagororin ma'aikatu, da ma bangaren shari'a, game da ayyukan hadin gwiwa domin tabbatar da tsaro.
Shugaban na Burundi ya kuma ce za a aiwatar da wata manufa da za ta wajibtawa matasa gudanar da ayyukan bautawa kasa musamman a jami'o'i. Yayin da kuma a daya hannu za a ci gaba da dora muhimmanci ga cusa kishin kasa a zukatun al'umma, matakin da a cewar shugaban na Burundi zai tallafa wajen kiyaye tsaro, da bunkasa zaman lafiya a kauyuka da alkaryu.
Ya kara da cewa, manufofin gwamnatin tasa cikin shekarun 5 masu zuwa za su fi karkata ne ga inganta tsaro, da wanzar da zaman lafiya, da tabbatar da adalci. Sai kuma bunkasa tsarin dimokaradiyya, da kuma samar da ci gaba mai dorewa.(Saminu Alhassan)