in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai ga jami'an kasar Burundi
2015-08-05 10:28:53 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwa a jiya Talata 4 ga wata, wadda ke Allah wadai da harin da aka kai kan jami'ai biyu a kasar Burundi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka hallaka wani babban jami'i a ofishin shugaban kasar Burundi Adolphe Nshimirimana. Kuma a ranar Litinin aka kaiwa shugaban kungiyar kare wadanda aka tsare da su da tabbatar da hakkin dan Adam na kasar Pierre Claver Mbonimpa hari, lamarin da ya haddasa raunatar shugaban.

Sanarwar ta bayyana cewa, kwamitin sulhun bai amince da duk wani nau'i na irin wannan hari ba, kana ya yi kira ga daukacin bangarori daban daban na kasar Burundi da su kai zuciya nesa.

An dai samu aukuwar tashe-tashen hankula da keta hakkin dan Adam a yayin zaben shugaban kasar Burundi, kana yanayin tsaron kasar ya ci gaba da tsanantawa bayan zaben, lamarin da ya sa kwamitin sulhun damuwa matuka.

Kaza lika sanarwar ta kara da cewa, kwamitin sulhun ya yi kira ga gwamnatin kasar Burundi, da sauran bangarori daban daban da su koma teburin shawarwarin siyasa cikin hanzari. Kwamitin sulhun ya nuna goyon bayan sa ga kungiyoyin yankin dake goyon bayan shawarwari, musamman kungiyar raya kasashen gabashin Afirka, da kungiyar AU, kuma ya yi kira ga bangarori daban daban da su yi hakuri, su warware rikicin kasar ta Burundi ta hanyar siyasa. Kana kwamitin sulhun ya yi alkawarin ci gaba da goyon bayan Burundi wajen wanzar da zaman lafiya da zaman karko cikin dogon lokaci.

Adolphe Nshimirimana shi ne tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar Burundi, yana kuma aiki a ofishin shugaban kasar kafin a hallaka shi. Rahotanni sun nuna cewa ya taka muhimmiyar rawa, wajen kwantar da kura, a lokacin da ake tsaka da zanga-zangar nuna adawa da kudurin shugaba Nkurunziza na neman sake zama shugaban kasar.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa, wasu dakaru sanye da tufafin soja ne suka kaddamar da hari da na'urar harba Bam kan motar Nshimirimana.

A baya can dai Mbonimpa ya taba nuna kiyayya ga burin zarcewar Pierre Nkurunziza kan karagar mulkin kasar ta Burundi.

An ce wasu dakaru biyu dake kan babur ne suka budewa Mbonimpa wuta a ranar Litinin, wanda hakan ya sabbaba ji masa raunuka masu tsanani. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China