shugaba Nkurunziza ya bayyana wannan mataki ne da yammacin jiya Lahadi, yana mai cewa daukacin kasar Burundi na cikin halin jimamin kisan Nshimirimana.
Nkurunziza ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan aikin tsohon jami'in. Ya ce Nshimirimana ya bada gagarumar gudummawa wajen saita alkiblar harkokin tsaron Burundi tun daga shekarar 2003.
A daya bangaren kuma shugaba Nkurunziza ya yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan dake ritsawa da rayukan manyan jami'an kasar, yana mai jaddada bukatar kara kaimi wajen shawo kan matsalar.
Shaidun gani da ido sun ce wasu mahara sanye da kayan sarki ne suka kaiwa motar Nshimirimana hari da bindigar harba Bam da safiyar jiya Lahadi, bayan su yi masa kwantan bauna a unguwar Kamenge dake wajen birnin Bujumbura fadar mulkin kasar. (Saminu Alhassan)