Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya bukaci shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, da ya tattauna da sauran sassa masu ruwa da tsaki dake kasar sa, domin kawo karshen rikicin siyasar dake addabar Burundi.
Kakakin MDD Stephane Dujarric ya rawaito Mr. Ban na bayyana rashin jin dadin sa, game da yawaitar kisan manyan jami'an gwamnatin Burundi a baya bayan nan, yana mai bayyana bukatar komawa teburin shawara bayan dakatar da hakan tun a ranar 19 ga watan Yulin daya gabata.
Kaza lika ya umarci mahukuntan Burundin da su yi hadin gwiwa da kungiyar kasashen Gabashin Afirka, wadda Uganda ke wakilta domin cimma nasarar shawarwarin.
Dujarric ya kara da cewa a ranar Laraba, Mr. Ban ya zanta ta wayar tarho da shugaba Nkurunziza, inda ya jaddada suka game da kisan Adolphe Nshimirimana, da ma wani yunkuri da aka yi na hallaka daya daga masu rajin kare hakkin dan Adam a kasar wato Pierre Clavier Mbonimpa.
Yunkurin kashe Mbonimpa dai na zuwa ne kwana guda bayan kisan Nshimirimana, lamarin da masu ruwa da tsaki ke ta kiraye-kiraye da a gudanar da bincike a kasan sa.(Saminu Alhassan)