Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Burundi, Pierre Claver Ndayicariye ya bayyana a wannan rana cewa, dan takarar jam'iyyar kiyaye karfin demokuradiyya dake rike da mulkin kasar Burundi, Pierre Nkurunziza ya lashe babban zaben kasar bisa kuri'u kashi 69.41 cikin 100 da aka kada. Za a mika sakamakon zaben ga kotun tsarin mulkin kasar, wadda za ta yanke shawarar fitar da sakamako na karshe cikin kwanaki 9 masu zuwa.
Bisa kundin tsarin mulkin kasar Burundi, ana fitar da shugaban kasar ta hanyar kada kuri'a. Tsawon wa'adin shugaban kasa shi ne shekaru 5, amma kuma ana iya sake wani wa'adi na biyu. A shekarar 2005, Pierre Nkurunziza ya zama shugaban kasar bisa zaben da majalisar dokokin kasar ta yi. A shekarar 2010 kuma, ya yi tazarce bisa zaben da jama'ar kasar suka yi. A watan Afrilun bana, jam'iyyar dake rike da mulkin kasar ta sake gabatar da Nkurunziza a matsayin dan takarar jam'iyyar, lamarin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, dalilin haka ne kuma, jam'iyyun adawa sun nuna rashin amincewarsu ta hanyar gudanar da zanga zanga a birnin Bujumbura, hedkwatar kasar, da ma haifar da tashe-tashen hankula, har ma da janyo wani yunkurin juyin mulkin soja a lokacin, amma ba tare da cimma nasara ba. (Fatima)