in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi ta kori wani jami'in diplomasiyyar Rwanda
2015-10-09 10:23:43 cri
Gwamnatin kasar Burundi ta dauki wani mataki a ranar Laraba na tusa keyar babban mai ba da shawara na ofishin jakadancin Rwanda, mista Desire Nyaruhirira, zuwa kasarsa domin kaucewa, a cewar kakakin gwamnatin Burundi, kokarin da yake yana gurbata huldar dake tsakanin kasashen biyu.

A yayin da wani jami'in diplomasiyya ya zama mai laifi ko da wata halayyar dake sabawa wasu ka'idojin da aka amince a cikin yarjejeniyar kasa da kasa dake shafar harkokin diplomasiyya, sannan kuma aka sanar masa da laifinsa, don haka yana da kyau ya koma kasarsa domin kada ya lalata dangantaka tsakanin gwamnatin Burundi da kasar da yake wakilta, in ji kakakin gwamnatin, Philippe Nzobonariba a gidan rediyon kasa a ranar Alhamis. (Maman Ada)

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China