Shugaban Burundi ya yi alla wadai da kisan tsohon manjo janar
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya yi alla wadai da babbar murya a ranar Lahadi kan kisan tsohon shugaban rundunar sojojin Burundi, kanal mai ritaya Jean Bikomagu. Mista Nkurunziza ya yi wani kira ga dukkan daukacin 'yan kasar Burundi da kuma iyalan mamacin da su kasance kullum cikin hadin kai, da kuma kaucewa fadawa tarkon mahasada wanda burin su shi ne na tura kasar cikin tashin hankali. Haka kuma shugaban ya ba da wani wa'adi na kwanaki bakwai ga hukumomin da abin ya shafa domin an cafke wadanda suka aikata wannan kisa tare da gurfanar da su gaban kotu. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku