Muna godewa wasu kungiyoyin bada lamuni da dama dake taimakonmu wajen samun ci gaba, amma kuma muna alla wadai da wasu daga cikin irin wadannan kungiyoyin dake son ba da taimakon dake raba kan 'yan Burundi. Ba mu bukatar taimakon dake raba kan 'yan kasa, muna son taimakon da ba zai lalata hadin kan 'yan Burundi ba, in ji Pierre Nkurunziza a birnin Gitega dake tsakiyar kasar a yayin bikin rantsar da mambobin kwamitin CNDI. (Maman Ada)