Gwamnatin Burundi ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta amince da cigaban da ta samu
Gwamnatin kasar Burundi ta gudunar da wani taron musayar ra'ayi tare da jami'an diplomasiyya dake wannan kasa a ranar Labara, inda ta bukace su da su mara mata baya domin gamayyar kasa da kasa ta amince da cigaban da kasar Burundi ta samu tun bayan zabukan shekarar 2015.
Gwamnatin kasar na yin kira ga gamayyar kasa da kasa domin ta sake duba matsayinta, ta amince da cigaban da aka samu da kuma tallafawa kokarin hukumomin kasar da suke cigaba da yinsa, domin cigaban al'ummar Burundi, in ji Gaston Sindimwo, mataimakin shugaban kasa na farko. (Maman Ada)