in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka halaka sakamakon girgizar kasa a Afghanistan da Pakistan ya karu
2015-10-28 10:41:57 cri
Girgizar kasa mai tsanani da ta auku a yankin Hindu Kush dake arewa maso gabashin Afghanistan ta halaka mutane 115 yayin da wasu 500 suka jikkata a kasar. Haka kuma, a makwabciyarta, wato Pakistan, bala'in ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 248, yayin da wasu 1665 suka ji rauni. Jami'an kasashen biyu sun bayyana cewa, wurin da bala'in ya auku akwai duwatsu da yawa kuma yana da nisa daga birane, dalilin haka ne akwai matukar wuya wajen gudanar da ayyukan ceto yadda ya kamata ko ma kimanta yawan asarar da bala'in ya janyo.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayyana a ran 27 ga wata cewa, gwamnatin kasar Sin za ta baiwa kasashen biyu tallafi bisa bukatunsu, kungiyar Red Cross kuma za ta samar da tallafin gaggawa.

Ban da wannan kuma, Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya bugawa shugabannin kasashen biyu Ashraf Ghani Ahmadzai da Mamnoon Hussain wayar tarho, a madadin gwamnati da jama'ar Sin Mista Xi ya isar da juyayinsa game da asarar rayukan da aka samu a kasashen biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China