in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya mika sakon alhini ga takwaransa na Pakistan
2014-12-17 20:07:24 cri
A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon alhini ga takwaransa na kasar Pakistan Mamnoon Hussain, sakamakon mummunan harin ta'addanci da aka kai kan wata makaranta a kasar, wanda ya haddasa jikkata da kuma rasuwar mutane da dama.

Cikin sakon, a madadin gwamnatin da jama'ar kasar Sin shugaba Xi Jinping ya mika ta'aziya da sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata sakamkon wannan hari.

Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ta yi kakkausar suka kan duk wani nau'in ta'addanci da kuma wannan harin da aka kai a kasar ta Pakistan. Jama'ar kasar Sin na jajantawa al'ummomin kasar Pakistan sosai, haka kuma, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan kasar Pakistan kan yaki da ta'addanci.

Shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang ya mika wa takwaransa na kasar Pakistan Mian Muhammad Nawaz Sharif sakon alhini dangane da wannan lamarin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China