A wannan rana, yayin da kakakin gwamnatin lardin Balochistan ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, yankin Awaran na lardin ya kasance wurin da ya fi fama da bala'in, abin da ya riga ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 260, tare da jikkatar wasu sama da 300, sannan daruruwan gidaje sun rushe.
A wasu wurare na lardin kuma mutane 68 sun rasu, wasu sama da 100 kuma suka jikkata, kana gidaje da dama sun rushe. A cikin birnin, an riga an ceci wadanda suka jikkata, amma a yankunan karkara, an samu cunkoson motoci sakamakon girgizar kasa, shi ya sa, ma'aikata masu agaji ba su iya isa wuraren da bala'in ya shafa ba, bala'in na ci gaba da tsananta. Yanzu, gwamantin da sojojin kasar da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sun shiga cikin aikin ba da agaji.
Wani jami'in yankin Awaran ya fada wa kafofin yada labaru cewa, mutane kimanin dubu 280 suna fama da bala'in, abinda ya kawo karancin kayayyaki da aikin jinya a wurin, ya zuwa yanzu, bangaren soja na kasar ya riga ya aika da mutane kimanin 1600 zuwa yankunan Awaran da Khuzdar, wato inda aka fama da bala'in sosai, don gudanar da aikin ceto kana kuma sun samar da abinci da magunguna da tunana da dama.(Bako)