in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen da bala'in girgizar kasa a Pakistan ya hallaka sun kai 348
2013-09-26 15:11:29 cri

Adadin mutanen da bala'in girgizar kasa ya rutsa da su a Pakistan a ranar Talatan nan sun kai 348 dalilin gano wassu sabbin gawawwaki guda 20 da ma'aikatan ba da ceto suka yi a wurin da hakan ya faru.

Kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ba da labari, Abdul Rasheed Gadozai, mataimakin kwamishinan yankin Awaran inda bala'in ya fi kawo barna ya sanar da cewa, an gano gawawwaki guda 20 din ne a wani ginin da ya rufza a Mashkai, wani kauye dake yankin Awaran a daren Laraban nan.

Kafin wannan, wato da misalin karfe 6 da rabi na yammacin ranar Laraba, agogon kasar, mutane 328 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wannan bala'i, sannan guda 445 suka samu rauni, a bayanin da hukumar samar da agajin gaggawa ta kasar ta bayyana a cikin wata sanarwa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China