in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 20 sun mutu sakamakon harin bom da aka kai a wani masallaci a Pakistan
2015-01-30 20:36:24 cri

Kafofin yada labaru na kasar Pakistan sun labarta a yau Jumma'a da yamma 30 ga wata cewa, an kai harin bom kan wani masallacin 'yan darikar Shia a yankin Shikarpur na lardin Sindh da ke kudancin kasar, inda a kalla mutane 20 suka rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 40 suka jikkata.

Bayan harin, 'yan sanda da ma'aikatan ba da agaji sun isa wurin da harin ya abku cikin sauri. Yanzu an kai wadanda suka jikkata asibiri domin ba su jinya.

Firaministan Pakistan Mian Muhammad Nawaz Sharif ya yi tir da harin, tare da bukatar hukumomin da abin ya shafa da su bai wa wadanda suka jikkata jinya yadda ya kamata.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya ko wani mutum da ya dauki alhakin kai harin. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China