Gwamnatin kasar Pakistan ta ba da labari cewa, jiya Talata 24 ga wata da yamma, an yi girgirzar kasa mai karfi digiri 7.8 bisa Ma'aunin Ritcher a kudu maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 238, yayin da wasu fiye da 200 suka jikkata. Ban da haka, wani karamin tsibiri ya bullo sakamakon bala'in.
An ba da labari cewa, ba'ain ya auku ne a karfe 4 da minci 29 da yamma a yankin Awaran dake da nisan kilomita 600 daga kudu maso yammacin birnin Quetta hedkwatar lardin Baluchistan, kuma wannan girgizar kasa ta samu asili ne karkashin kasa na zurfi kilomita 20. Wani jami'in kasar ya bayyana cewa, yanzu an tura rukunonin aikin jiyya da sojoji 200 da dai sauran rundunonin soja da ba bisa ka'ida ba zuwa wurin. Akwai gine-gine da dama suka rufta, saboda haka, adadin asara zai karu.
Dadin dadawa, saboda girgizar kasa mai tsanani, shi ya sa wani karamin tsiribi ya bullo cikin tekun Arabia dake da nisan mita 600 daga tashar jiragen ruwa ta Gwadar da kasar Sin take kula da harkokinta. (Amina)