in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gurfanar da tsohon shugaban Pakistan a kotu a karo na farko
2014-02-19 17:16:23 cri
Tsohon shugaban kasar Pakistan Pervez Mushharaf ya gurfana a kotun musamman karo na farko a ran 18 ga wata, don sauraron tuhumar da ake yi masa dangane da laifin cin amanar kasa.

Lauyan da ke kare Mr. Mushharaf ya bayyana cewa, kotun ba ta da ikon hukunta Mr. Mushharaf, sabo da a shekarar 2007, Mr. Mushharaf ya sanya dokar ta baci a matsayinsa na hafsan hafsoshin sojojin kasar Pakistan, ya kamata a hukunta shi a kotun soja.

A karshe, kotun musamman ba ta saurari karar da aka yi wa Pervez Mushharaf ba, inda ta bayyana cewa, za ta tsai da kuduri kan ko kotun masamman na da ikon hukunta Pervez Mushharaf, ko a'a cikin wannan mako. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China