in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ta'aziyar wadanda suka rasu sakamakon harin ta'addanci a Pakistan
2014-12-17 20:41:41 cri
A yau Laraba 17 ga wata ne, aka yi ta'aziyar mutane guda 145 da suka rasu sakamakon harin ta'addanci da aka kai kan wata makaranta dake birnin Peshawar a kasar Pakistan. A wannan rana ne kuma, gwamnatin kasar Pakistan ta tsai da kudurin dawo da hukuncin kisa kan duk wadanda aka samu da aikata laifuffukan da suka shafi ta'addanci.

Haka kuma, dakarun Taliban dake kasar sun sanar da daukar alhakin harin, sun ce wannan harin ramuwar gayya ce kan harin da sojojin kasar suka kai ga dakarunsu, kana sun lashe takwabin ci gaba da kai karin hare-hare ga sojojin kasar ta Pakistan. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China