in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da harin ta'addanci a kasar Pakistan
2014-06-10 15:49:35 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayar da wata sanarwa ta hanyar kakakinsa, wacce ke dauke da Allah wadai da harin ta'addancin da aka kaddamar a kasar Pakistan, tare da bukatar tabbatar da hukunta masu hannu cikin wannan ta'asa.

Cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya nuna damuwa kwarai game da rikice-rikicen da ake samu a sassa daban daban na kasar Pakistan, ya kuma amince cewa, matakan da kasar ta dauka domin dakile hakan sun dace. Daga nan sai Mr. Ban ya kalubalanci gwamnatin kasar Pakistan, da ta kara kokarin tinkarar ta'addanci, da masu tsattsauran ra'ayin addinai, ta kuma cafke maharan ba tare da bata lokaci ba. Haka zalika, Ban Ki-moon ya jajantawa iyalan mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren, tare da bayyana goyon bayansa ga gwamnatin kasar da jama'arta.

A daren ranar 8 ga watan nan ne dai wasu dakaru dauke da makamai, suka kai hari filin sauka da tashin jiragen sama dake Karachi, inda daga bisani suka yi dauki ba dadi da sojojin tsaron filin da kuma 'yan sanda, lamarin da ya haddasa rasuwar daukacin maharan su 10.

Bugu da kari an ce an kaddamar da wani harin na daban kan ayarin motoci dake dauke da wasu 'yan Shi'a a yankin iyakar kasa dake jihar Baluchistan, a kudu maso yammacin kasar Pakistan a daren ranar Lahadi, harin da shi ma ya sabbaba mutuwar mutane a kalla 30. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China