Rahotanni dai sun bayyana cewa an kai harin ne kan wani masallacin 'yan Shi'a dake yankin Shikarpur dake lardin Sindh dake kudancin kasar.
'Yan sanda sun ce mutane da dama sun rasu sakamakon rufzawar da masallacin ya yi a kansu. Sun ce bam din ya tashi lokacin da kimanin mutane 600 ke salla cikin masallacin.
Bayanai na cewa mai iyuwa ne adadin mutane da harin ya hallaka ya ci gaba da karuwa, sakamakon matsanancin hali da wasu wadanda harin ya ritsa da su ke ciki yanzu haka.
Kawo yanzu dai gwamnatin kasar ba ta ce komai game da harin ba tukuna, sai dai kafofin watsa labaran yankin sun labarta cewa, wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta 'yan Sunni mai suna Jundallah, ta sanar da daukar alhakin kai harin, kungiyar da tun bara ta bayyana mubaya'ar ta ga kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama. (Maryam)