Narendra Modi zai yi rantsuwar kama aiki a ranar 26 ga wata, tun bayan da aka bada sakamakon babban zabe a kasar Indiya. Kafin wannan, jam'iyyar Bhartiya Janta ta Indiya (BJP) ta mista Modi ta bayyana cewa, Indiya ta riga ta gayyaci shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta shiyya-shiyya ta kudancin Asiya(SAARC)domin halartar bikin kama aikin mista Modi, ciki har da kasar Pakistan.
Indiya da Pakistan sun taba yin yaki sau uku tsakaninsu cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, kuma a kan samu rikici tsakanin kasashen biyu game da yankin Kashmir, lamarin dake kara tsananta yanayin dangantakar kasashen biyu. A shekarar bara, firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya taba gayyatar tsohon firaministan Indiya Manmohan Singh domin ya halarci bikin kama aikinsa, amma ba tare da samun nasarar zuwan takwaransa na Indiya ba.